DA ƊUMI-ƊUMI: Lokaci Ya Yi Da Za Mu Kawo Sauyi A Najeriya, Cewar Shugaban Jam’iyyar PDP Na Ƙasa Ambasada Umar Iliya Damagun

Shugaban riƙon jam’iyyar (PDP) na ƙasa, Ambasada Umar Iliya Damagun ya koka kan yadda jam’iyyar (APC) mai mulki ta ke ƙoƙarin yi wa dimokaraɗiyya fyaɗe a Jihohin da ake gudanar da zaɓen gwamna domin ta ƙwace iko da Jihohin.

Damagun ya bayyana hakan ne ta cikin tattaunawarsa da Jaridar Dokin Ƙarfe TV a garin Gulak na ƙaramar hukumar Madagalin Jihar Adamawa a yau, kamar yadda ya ce "Bayan zaɓen Jihar Edo, abin kunya shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya fito ƙarara yana iƙirarin cewa za su yi amfani da ƙarfi su ƙwaci zaɓi a Jihohin Osun da Ondo duk da irin halin damuwa da ƙunci da ake ciki a ƙasar nan". Inji shi.

Ya cigaba da cewa "Mutane suna fama da yunwa da tsadar kayan masarufi da taɓarɓarewar tsaro, amma duk da wannan hali da ake ciki mutum ya fito yana cewa wai za su ƙwace zaɓe a wasu Jihohi ko da ba ta bin tsarin dimokaraɗiyya ba ne. Amma ban yi mamaki ba tunda sun san cewar in ba hakan suka yi ba jama’a ba za su zaɓe su ba". Inji Damagun.

Dmagun, ya kuma ƙara da yin kira ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro da su tabbatar da adalci kan kowa. Kamar yadda ya ce, "Najeriya ta kowa ce, kuma al’ummar Osun sun cancanta su samu zaman lafiya a kuma ba su abin da suke so. Ina kira ga jami’an tsaro da su daina karkata kan ba wa wata jam’iyya kariya domin da haƙƙin kowane ɗan ƙasa na haraji ake biyan su albashi. Kowane ɗan ƙasa yana da yancin bayyana ra’ayinsa da zaɓar abin da yake so". Kamar yadda ya bayyana.

Daga nan ya kuma nemi ƴan Najeriya da su guji amsar abin da bai taka kara ya karya ba a zaɓen 2027 domin su tserar da kan su daga ƙangin bautar da (APC) ta jefa su. "Duk da cewa akwai saɓani da rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP, amma dai jam’iyya ce da ta fi kowa ƙarfi, babu mai iya ganin bayanta. Jam’iyyar APC jam’iyya ce marar manufa, ko da a zaɓen 2023 mun faɗa cewa ba abin da suke son su cimma face su saci ƙuri’un jama’a su hau mulki, ba su shirya yin komai ba, dan haka yanzu lokaci ne da za mu karɓe mulki mu kawo sauyi". Inji shugaban jam’iyyar PDP ta ƙasa Ambasada Umar Iliya Damagun.

Menene ra'ayinku?
DA ƊUMI-ƊUMI: Lokaci Ya Yi Da Za Mu Kawo Sauyi A Najeriya, Cewar Shugaban Jam’iyyar PDP Na Ƙasa Ambasada Umar Iliya Damagun Shugaban riƙon jam’iyyar (PDP) na ƙasa, Ambasada Umar Iliya Damagun ya koka kan yadda jam’iyyar (APC) mai mulki ta ke ƙoƙarin yi wa dimokaraɗiyya fyaɗe a Jihohin da ake gudanar da zaɓen gwamna domin ta ƙwace iko da Jihohin. Damagun ya bayyana hakan ne ta cikin tattaunawarsa da Jaridar Dokin Ƙarfe TV a garin Gulak na ƙaramar hukumar Madagalin Jihar Adamawa a yau, kamar yadda ya ce "Bayan zaɓen Jihar Edo, abin kunya shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya fito ƙarara yana iƙirarin cewa za su yi amfani da ƙarfi su ƙwaci zaɓi a Jihohin Osun da Ondo duk da irin halin damuwa da ƙunci da ake ciki a ƙasar nan". Inji shi. Ya cigaba da cewa "Mutane suna fama da yunwa da tsadar kayan masarufi da taɓarɓarewar tsaro, amma duk da wannan hali da ake ciki mutum ya fito yana cewa wai za su ƙwace zaɓe a wasu Jihohi ko da ba ta bin tsarin dimokaraɗiyya ba ne. Amma ban yi mamaki ba tunda sun san cewar in ba hakan suka yi ba jama’a ba za su zaɓe su ba". Inji Damagun. Dmagun, ya kuma ƙara da yin kira ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro da su tabbatar da adalci kan kowa. Kamar yadda ya ce, "Najeriya ta kowa ce, kuma al’ummar Osun sun cancanta su samu zaman lafiya a kuma ba su abin da suke so. Ina kira ga jami’an tsaro da su daina karkata kan ba wa wata jam’iyya kariya domin da haƙƙin kowane ɗan ƙasa na haraji ake biyan su albashi. Kowane ɗan ƙasa yana da yancin bayyana ra’ayinsa da zaɓar abin da yake so". Kamar yadda ya bayyana. Daga nan ya kuma nemi ƴan Najeriya da su guji amsar abin da bai taka kara ya karya ba a zaɓen 2027 domin su tserar da kan su daga ƙangin bautar da (APC) ta jefa su. "Duk da cewa akwai saɓani da rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP, amma dai jam’iyya ce da ta fi kowa ƙarfi, babu mai iya ganin bayanta. Jam’iyyar APC jam’iyya ce marar manufa, ko da a zaɓen 2023 mun faɗa cewa ba abin da suke son su cimma face su saci ƙuri’un jama’a su hau mulki, ba su shirya yin komai ba, dan haka yanzu lokaci ne da za mu karɓe mulki mu kawo sauyi". Inji shugaban jam’iyyar PDP ta ƙasa Ambasada Umar Iliya Damagun. Menene ra'ayinku?
0 Comments ·0 Shares ·0 Reviews
Sponsored
Upgrade to Pro
Choose the Plan That's Right for You
Sponsored