SYRIA TA SHIGA WALA GIGI

Syria ta zama mace da ciki a wajen waɗanda suka tunkuɗe Asad, musamman Turkiyya da Qatar Sun rasa sanin ina aka dosa.

Bayyane ta koma ɓoye. Hatta Amrk batada matsaya kwara ɗaya a kan Sy*ria.

Mutum biyu ne kaɗai suka san me suke son yi a Syria kuma suka fara shirye-shiryen aikatawa, su ne Haramtacciyar ƙasar Is*ra'il*a da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Ɗayansu ne zai mallaki Sy*ria a nan gaba.

A gajeren Hasashe irin na wanda ke kallon abubuwa daga nesa, wanda ba lallai bane ya zamo daidai, ga dukkan alamu ita Isr*a'ila za ta kafa iko na wacin gadi a Sy*ria kafin daga baya mazajen Kararru su mata zuwa guda. Duka ɗauka za a mata a Syria, ba taf-taf-taf za a tsaya a na yi ba. Amma sai bayan sun gama nasu display ɗin irin na yan wasan Dandali.

Idan wannan hasashen ya tabbata, to zai zamo kenan a Syria aka fara Damben, kuma a nan ne za a buga final.

Jolani ƙwararren player ne da Amrk ta yaye a yammacin Iraqi a shekarun baya, kafin. Ya zamo karen Hukumar leken Asiri Turkawa. Yanzu kuma da ya samu iko ya fara bugun Kaki yana bugun taiki. Ga dukkan alamu Turkiyya ta fara hattara da shi, saboda basu gane motsinsa ba. Ba abun mamaki bane a nan gaba Kare ya juya ya ciji masu gidansa. Butulallen Mahalbi zai kiran gasar halbi da wanda ya kowa masa riƙe Baka. Dama dai shi ramin ƙarya ƙurarre ne.

Mu je zuwa wai Mahaukaci ya hau kura...

Shamsudeen Hassan Zuru
SYRIA TA SHIGA WALA GIGI Syria ta zama mace da ciki a wajen waɗanda suka tunkuɗe Asad, musamman Turkiyya da Qatar😀 Sun rasa sanin ina aka dosa. Bayyane ta koma ɓoye. Hatta Amrk batada matsaya kwara ɗaya a kan Sy*ria. Mutum biyu ne kaɗai suka san me suke son yi a Syria kuma suka fara shirye-shiryen aikatawa, su ne Haramtacciyar ƙasar Is*ra'il*a da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Ɗayansu ne zai mallaki Sy*ria a nan gaba. A gajeren Hasashe irin na wanda ke kallon abubuwa daga nesa, wanda ba lallai bane ya zamo daidai, ga dukkan alamu ita Isr*a'ila za ta kafa iko na wacin gadi a Sy*ria kafin daga baya mazajen Kararru su mata zuwa guda. Duka ɗauka za a mata a Syria, ba taf-taf-taf za a tsaya a na yi ba. Amma sai bayan sun gama nasu display ɗin irin na yan wasan Dandali. Idan wannan hasashen ya tabbata, to zai zamo kenan a Syria aka fara Damben, kuma a nan ne za a buga final. Jolani ƙwararren player ne da Amrk ta yaye a yammacin Iraqi a shekarun baya, kafin. Ya zamo karen Hukumar leken Asiri Turkawa. Yanzu kuma da ya samu iko ya fara bugun Kaki yana bugun taiki. Ga dukkan alamu Turkiyya ta fara hattara da shi, saboda basu gane motsinsa ba. Ba abun mamaki bane a nan gaba Kare ya juya ya ciji masu gidansa. Butulallen Mahalbi zai kiran gasar halbi da wanda ya kowa masa riƙe Baka. Dama dai shi ramin ƙarya ƙurarre ne. Mu je zuwa wai Mahaukaci ya hau kura... Shamsudeen Hassan Zuru
0 Comments ·0 Shares ·0 Reviews
Sponsored
Upgrade to Pro
Choose the Plan That's Right for You
Sponsored