ƘARIN HASKE SS (86): FITO-NA-FITO TSAKANIN GA*ZA DA MAHAUKACIN KARE MAI CIZO(11)

Dangane da batun tura Falasɗinawa zuwa Saharar Sinai, jiya Shugaban Misira Sisi ya yi magana. Amma a cikin maganarsa babu mutunci ko na Sisin kwabo a cikinta, babu tausayi, babu nuna rahama ko kaɗan zuwa ga raunanan Falasɗinawa. Son kai ne a cikin jawabinsa zalla.

Amma duk da haka matsayarsu za ta amfani mihwarul muƙawama. Sisi ya gasgata Hasashen da Ƙarin Haske ya kwashe shekara yana yi dangane da matsayar Misira a wannan rikicin.

Ga abunda Sisi yace:

“Mayarda Falasɗinawa zuwa Saharar Sinai, tamkar mayarda fikirar resistance axis da yaƙi ne zuwa wajen. Yin haka zai bawa Is*ra’ila dama ta kaiwa iyakokin Misira hari da sunan daƙile yan gwagwarmaya, da sunan kare kanta. To ai sunada Saharar Negev, Is*ra’ila ta turasu a can mana”.

A cikin wannan maganar akwai manyan abubuwa guda ukku:

1. Matsayar Misira a kan wannan rikicin shine, su ba ruwansu ko da Isr*a’ila za ta kashe kowa a Ga*za, domin wannan ba matsalar Egypt bane. Amma basu yadda a kashesu a cikin iaykokinsu ba, ba domin suna tausayinsu ba, sai domin kada wannan yasa Is*ra’ila ta mamayi yankinsu.

2. Sisi da rundunarsu ta Misra, suna da masaniyar me ake ƙoƙarin kullawa, sun san manufar Mahaukacin Kare na mayarda Gaza babban wajen shakatawa a yammacin Asiya , to wannan ba damuwarsu bace, damuwarsu kada a taɓa masu Sinai ɗinsu.

3. A cikin jawabinsa akwai nuna isa da ƙarfi wanda sojojin Misira ke da shi, idan ana magana dangane da saɓanin da ke tsakaninsu da Is*ra’ila. Duk da cewa da Sisi da Na tan yaaa hooo duk yan club ɗaya ne, amma akwai inda suka rabu, shine batun taɓa iyakokin Misira, iyakokin da sojojin amfani da su wajen ci gaba da shugabanci a Egypt.

Misrawa na ganin sojojinsu a matsayin manyan Gwaraza ne saboda sun yaƙi Isra’ila sun kwato Sinai a hannunsu a shekarun baya. To idan Sisi ya yi wasa, wannan siƙar ta fita, to al’umma za su bar ganinsu a matsayin Gwaraza, wannan zai iya haifar da samun sauyi Na Asali a Egypt.

To a wajen sojojin Misira Gara su gwabza yaƙi da Isra’ila da ace sun barta ta zubar masu da kima ba tare da an yi yaƙi ba. Wato kin amincewar ba domin tausayi bane, magana ce ta kariyar kai.

Amma duk da haka, wannan zai amfani gwagwarmayar Falasɗinawa, kamar yadda ya mafanesu a sadda ake yaƙi. Idan Misira ta dage a kan wannan matsayar, su kuma Falasɗinawa suka dage da Tirjiya a cikin gida, to dole a bar masu kayansu,a bar masu gazarsu.

Idan kuma Misira ta kasa jurewa matsin lambar Mahaukacin Kare ta ƙara masu tarrifs da janye masu tallafi, to wannan zai bawa Mahaukacin Kare damar ƙara kuzari wajen ganin ya kori Falasɗinawa daga G*aza.

Har yanzu dai ta wannan janibin Misira ce za ta taka rawa,koda kuwa rawar ta son Kai ce. Dama su aƙidar yan ƙasanci ne ke gudana a cikin jijiyoyinsu ba kishin addini ba. Iyakokin Misira ne Holly na farko a cikin tsarin sojojinsu ba masallacin Qudus ba.

Wannan matsayar da Misira ke ɗauka idan ana maganar iyakokinta shine dalilin da yasa hatta ita kanta Misra suke son gamawa da ita a nan gaba. Kamr yadda Ƙarin Haske Sabo shafi na 78 ya yi bayani.

To fatanmu shine su yi tsaye a kan wannan ra’ayin duk da akwai rashin tausayin Falasɗinawa a cikinsa, domin cewa a kaisu Saharar Negev da Sisi yayi, shine gayar rashin tausayi da rashin mutunci da cin fuska zuwa ga raunanan Ga*za.

Wannan hanyar ta Tirjiya domin ƙasa,kamar yadda Misirawa suke yi, ko domin Qudus kamar yadda resistance axis ke yi, itace hanya ta biyu ta yakar wannan lamari.

Ƙarin bayani zai zo insha’Allah .

Shamsudeen Hassan Zuru
29/1/2025
ƘARIN HASKE SS (86): FITO-NA-FITO TSAKANIN GA*ZA DA MAHAUKACIN KARE MAI CIZO(11) Dangane da batun tura Falasɗinawa zuwa Saharar Sinai, jiya Shugaban Misira Sisi ya yi magana. Amma a cikin maganarsa babu mutunci ko na Sisin kwabo a cikinta, babu tausayi, babu nuna rahama ko kaɗan zuwa ga raunanan Falasɗinawa. Son kai ne a cikin jawabinsa zalla. Amma duk da haka matsayarsu za ta amfani mihwarul muƙawama. Sisi ya gasgata Hasashen da Ƙarin Haske ya kwashe shekara yana yi dangane da matsayar Misira a wannan rikicin. Ga abunda Sisi yace: “Mayarda Falasɗinawa zuwa Saharar Sinai, tamkar mayarda fikirar resistance axis da yaƙi ne zuwa wajen. Yin haka zai bawa Is*ra’ila dama ta kaiwa iyakokin Misira hari da sunan daƙile yan gwagwarmaya, da sunan kare kanta. To ai sunada Saharar Negev, Is*ra’ila ta turasu a can mana”. A cikin wannan maganar akwai manyan abubuwa guda ukku: 1. Matsayar Misira a kan wannan rikicin shine, su ba ruwansu ko da Isr*a’ila za ta kashe kowa a Ga*za, domin wannan ba matsalar Egypt bane. Amma basu yadda a kashesu a cikin iaykokinsu ba, ba domin suna tausayinsu ba, sai domin kada wannan yasa Is*ra’ila ta mamayi yankinsu. 2. Sisi da rundunarsu ta Misra, suna da masaniyar me ake ƙoƙarin kullawa, sun san manufar Mahaukacin Kare na mayarda Gaza babban wajen shakatawa a yammacin Asiya , to wannan ba damuwarsu bace, damuwarsu kada a taɓa masu Sinai ɗinsu. 3. A cikin jawabinsa akwai nuna isa da ƙarfi wanda sojojin Misira ke da shi, idan ana magana dangane da saɓanin da ke tsakaninsu da Is*ra’ila. Duk da cewa da Sisi da Na tan yaaa hooo duk yan club ɗaya ne, amma akwai inda suka rabu, shine batun taɓa iyakokin Misira, iyakokin da sojojin amfani da su wajen ci gaba da shugabanci a Egypt. Misrawa na ganin sojojinsu a matsayin manyan Gwaraza ne saboda sun yaƙi Isra’ila sun kwato Sinai a hannunsu a shekarun baya. To idan Sisi ya yi wasa, wannan siƙar ta fita, to al’umma za su bar ganinsu a matsayin Gwaraza, wannan zai iya haifar da samun sauyi Na Asali a Egypt. To a wajen sojojin Misira Gara su gwabza yaƙi da Isra’ila da ace sun barta ta zubar masu da kima ba tare da an yi yaƙi ba. Wato kin amincewar ba domin tausayi bane, magana ce ta kariyar kai. Amma duk da haka, wannan zai amfani gwagwarmayar Falasɗinawa, kamar yadda ya mafanesu a sadda ake yaƙi. Idan Misira ta dage a kan wannan matsayar, su kuma Falasɗinawa suka dage da Tirjiya a cikin gida, to dole a bar masu kayansu,a bar masu gazarsu. Idan kuma Misira ta kasa jurewa matsin lambar Mahaukacin Kare ta ƙara masu tarrifs da janye masu tallafi, to wannan zai bawa Mahaukacin Kare damar ƙara kuzari wajen ganin ya kori Falasɗinawa daga G*aza. Har yanzu dai ta wannan janibin Misira ce za ta taka rawa,koda kuwa rawar ta son Kai ce. Dama su aƙidar yan ƙasanci ne ke gudana a cikin jijiyoyinsu ba kishin addini ba. Iyakokin Misira ne Holly na farko a cikin tsarin sojojinsu ba masallacin Qudus ba. Wannan matsayar da Misira ke ɗauka idan ana maganar iyakokinta shine dalilin da yasa hatta ita kanta Misra suke son gamawa da ita a nan gaba. Kamr yadda Ƙarin Haske Sabo shafi na 78 ya yi bayani. To fatanmu shine su yi tsaye a kan wannan ra’ayin duk da akwai rashin tausayin Falasɗinawa a cikinsa, domin cewa a kaisu Saharar Negev da Sisi yayi, shine gayar rashin tausayi da rashin mutunci da cin fuska zuwa ga raunanan Ga*za. Wannan hanyar ta Tirjiya domin ƙasa,kamar yadda Misirawa suke yi, ko domin Qudus kamar yadda resistance axis ke yi, itace hanya ta biyu ta yakar wannan lamari. Ƙarin bayani zai zo insha’Allah . Shamsudeen Hassan Zuru 29/1/2025
0 Comments ·0 Shares ·0 Reviews
Sponsored
Upgrade to Pro
Choose the Plan That's Right for You
Sponsored