An sakawa Zakanya sunan 'Ladi' a Kano domin girmamawa ga iyalan Marigayi Audu Bako
A wani babban bikin tunawa da tarihin marigayiya Hajiya Ladi Audu Baƙo, wacce ita ce uwargidan gwamna ta farko kuma ginshikin kafuwar Gidan adana Namun Daji na Kano (Kano Zoological Garden), an sanya wa wata ‘ƴar zaki suna “Ladi” don tunawa da ita.
Bikin sanya sunan, wanda aka yi a Gidan adana Namun Daji na Kano, ya samu halartar tsohuwar shugabar Gidan, Hajiya Zainab Audu Bako, wacce ta wakilci dangin Audu Bako.
Taron ya gudana ne bisa sahalewar gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda shugaban hukumar Gidan, Hon Sadiq Kura Muhammad, ya jagoranta a ranar Talatar da ta gabata.
~ Nasara Radio

0 Comments
0 Shares
0 Reviews