Sponsored
An Yi Wa ‘Yar Shekara 2 Fyaɗe Har Ta Mutu A Bauchi

https://hausa.leadership.ng/an-yi-wa-yar-shekara-2-fya%c9%97e-har-ta-mutu-a-bauchi/
An Yi Wa ‘Yar Shekara 2 Fyaɗe Har Ta Mutu A Bauchi https://hausa.leadership.ng/an-yi-wa-yar-shekara-2-fya%c9%97e-har-ta-mutu-a-bauchi/
HAUSA.LEADERSHIP.NG
An Yi Wa ‘Yar Shekara 2 Fyaɗe Har Ta Mutu A Bauchi
Wata yarinya ƙarama ‘yar shekara biyu aka samu rahoton cewa, an yi mata fyaɗe har ta rigamu gidan gaskiya, kana ya jefar da gangar jikinta a gefen wani masallaci a ƙaramar hukumar Ningi da ke jihar Bauchi. A wata sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar Bauchi (PPRO) Sufuritandan Ɗansa, Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Talata, ya ce, tawagar ‘yansanda sun isa wurin da aka samu rahoton faruwar lamarin domin nemo bayanin abun da ya faru da kuma bincike. Ya ce: “A ranar 5 ga watan Nuwamban 2024, an kai rahoton ga caji ofis ɗin ‘yansanda da ke Ningi inda aka taras da gangar jikin wata yarinya ‘yar shekara biyu amma ba ta motsi sam-sam a gefen wani masallaci da ke layin Deneva a cikin ƙaramar hukumar Ningi, sai dai alamun zargin an mata fyaɗe sun bayyana.” Ya yi bayanin cewa, an ɗauki gangar jikin yarinyar zuwa babban asibitin Ningi, inda a nan ne likita ya tabbatar da cewa, yarinyar ta gamu da raunuka ne sakamakon keta mata haddi da aka yi wanda har hakan ya yi ajalinta. Kwamishinan ‘yansandan jihar CP Muhammad Auwal Musa ya yi tir da wannan mummunar aika-aikar tare da umartar babban baturen ɗansanda (DPO) na Ningi da ya jagoranci gudanar da bincike na zahiri domin cafko masu hannu a wannan ɗanyen aikin domin tabbatar da sun fuskanci shari’a. Kazalika, ya buƙaci iyaye da masu kula da yara da suke tabbatar da kula da lafiya da tsaron ‘ya’yansu, kana suke daina barinsu suna yawo kwararo-kwararo ba tare da sanya ido ko kula ba. Kuma, ya nemi jama’a da su taimaka da dukkanin bayanin da za su kai ga cafko waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin domin ganin an ɗaɗana musu kuɗarsu.
0 Comments 0 Shares 0 Reviews
Sponsored
Sponsored
Sponsored
Sponsored