Idan kana bibiyar Siyasar gabas ta tsakiya da idon basira, ka san Syed Ali Al-Sistany yana zaune ne akan wutar fitintinu ya danne ta. Allah ya tsawaita mana rayuwar sa, yanzu shi ɗaya ne tilo da shirun sa ya rufe ƙofar barakar Iraqi da kewaye, rasa shi ba ƙaramar dambarwa zata haifar ba.
Zubi da Usulubin Marji'iyar sa ita ta dace da Iraqawa, kuma da wannan shirun ya sayi dukkan mutunci da girmamawa a idanun su, ƴan Siyasa ko Maluman Addini, sirrin ɗaukakar su shine raɓuwa da Sayyid.
Yanzu haka Amurka ta kunno wutar fitina akan sai an soke Rundunar su Shahid Haj Mahdi Al-Muhandis wato Hashd Al-Sha'abi, amma Sayyid Ali Sistany yaƙi amincewa, wadda rusa wannan runduna kamar dawo da ƙungiyoyin takfiriyya ne da ƙafafun su IRAQI, yanzu a wannan gaɓar Sayyid Ali ke tasa gwagwarmayar.
Ko ya makomar Iraqi zata kasance ba Sayyid? Wannan wani lamari ne da duk masu sharhin duniya basu da abin cewa akai, mace ce mai ciki ba'a san me zata haife ba. Allah ya tsawaita mana rayuwar sa, ya inganta masa lafiya.
— Muhammad Balaa Afuwaa