NASIHAR JAGORA (H) GA 'YAN UWA.....
"To kuma don Allah ‘yan uwa, a kauce wa irin abin da ake jefa mu a kai na maganganu, la’alla yamu-yamu ne tsakaninmu ne, ko kuma tsakaninmu da wasu. Don Allah a kauce wa wannan.
“Yamu-yamu dama kullum na kan wa ‘yan uwa magana nace in dai za ku yi aiki tare akwai matsala fa, haka abin ya gada. Za ka ji wani kai kana abinka tsakani da Allah, wani kuma bashi da wani aiki sai suka, wai kai dan bani na iya ne, kana wani nuna ka fi kowa ne, kai kaza-kaza.
"Oho dai, kana yi don wane ne? To ka yi abinka idan don Allah kake yi, amma idan domin shi (mai sukan) kake yi, sai ka bari tunda ya kwazzabeka ya dame ka, amma idan don Allah kake yi sai ka cigaba da abinka, ladanka na wajen Allah."
— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a yayin ganawa da wakilan yan uwa a ranar Asabar 9/10/1444 (29/4/2023) a gidansa da ke Abuja.