An Ɗaura Auren Ɗiyar Shaikh Shaheed Muhammad Turi (RA) Ta Shida (6)
Saifullahi M Kabir
4 Rajab 1446 (4/1/2025)
A safiyar yau Asabar 4 ga Rajab 1446 (4/1/2025) ne aka Ɗaura auren Dr. Sukainah Muhammad, ɗiya ta shida, kuma autar Shaikh Muhammad Mahmud Turi, da angonta Acct. Ja'afar Ibrahim, a Markaz din 'yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na Kano.
Allah Ta'ala Ya azurta Shaikh Muhammad Turi da haihuwar 'ya'ya mata ne guda shida, kafin Shahadarsa a Waki'ar Buhari ta 2015 a Zariya, Shahid Muhammad Turi ya aurar da huɗu daga 'ya'yan nasa, kuma cikin nufin Allah Ta'ala bayan Shahadar, aka yi auren ragowar biyun; Hakima, da kuma Sukainah da aka daura nata a yau.
Kamar yadda aka shaida min, dama Shaikh Muhammad Turi yana wakilta amininsa Shaikh Yakubu Yahya ne wajen ba da auren duk 'ya'yansa da suka gabata tun yana raye, don haka ko bayan bashi ma, Iyalan Shaikh din, da 'yan uwansa na jini, ciki har da yayansa Alhaji Ali Turi, sun danka al'amarin ne ga Shaikh Yakubu Yahya, wanda ya wakilci amaryar wajen ba da aurenta.
Auren ya samu halartan dimbin al'umma, dangi na jini, da 'yan uwa na addini, da abokan arziki daga gidajen Ƙadiriyya da Tijjaniyya na garin Kano.
Abin taya murna ne kwarai ga Shaheed Muhammad Turi da maidakinsa Malama Maimuna Abdullahi, na cewa Allah Ta'ala Ya azurta su da zallan 'ya'ya mata har shida, kuma sun tsayu sosai wajen ganin sun tarbiyantar da su tare da ilmantar da su, sannan dukkansu Allah Ya basu ikon aurar da su cikin aminci. Wanda akwai ruwayoyi masu yawa da suke bayanin falalar wanda Allah Ya ba 'ya mace ya ilmantar da ita tare da tarbiyantarwa har ya kai ga aurar da ita ga miji nagari.
Muna kuma taya Jagoranmu (H) murna, tare da fatan Allah Ta'ala Ya yi masa dukkan sakayyar alheri, bisa ilimi da ya shayar, da tarbiyan da ya bayar, da kulawa ta musamman ga wannan amintacce nashi, masoyi na haƙiƙa, Shaheed Muhammad Turi. Babu shakka, mun ga karantarwar Jagora (H) a aikace a jikin Shaikh Turi ta kowane bangare. Allah Ta'ala Ya sa mu kasance misalin Shaikh Muhammad Turi a gare su ta fuskancin sadaukarwa da sallamawa ga addini.
Allah Ya sakawa duk wadanda suka samu halarta da alkairi. Ya sanya alkairinSa, Ya ba da zuriya tagari, alfarmar Annabi da Ahlulbaiti (AS).
— Saifullahi M Kabir