Shirin Yamma na 12/11/2024
Masu bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta ina muku barka da wannan lokacin.
Musa Tijjani Ahmad ne zai kasance da ku a shirinmu na maraice da karfe bakwai agogon Najeriya da Nijar, shida kenan agogon GMT da Ghana.
Ku latsa nan domin sauraronmu kai tsaye a babban shafinmu na intanet da zarar lokacin yayi
https://p.dw.com/p/15bt5
Ga jerin rahotannin da shirin ya kunsa.
1. Manyan jam'iyyun siyasar Jamus sun amince a gudanar da zaben wuri a ranar 23 ga watan Fabrairun shekara mai kamawa ta 2025.
2. Gwamnatin jihar Kebbi ta shirya wata babbar tawaga zuwa Abuja domin ganawa da shugaban hafsan tsaro don dakatar da ayyukan Lakurawa a jihar.
3. Al'ummar yankin Ogoni da ke kudancin Najeriya sun nuna farin ciki kan matakin gwamnatin Najeriya na karrama jagoran fafutukar yankin Ken Saro-Wiwa da kuma wasu mutum takwas.
4. An fara takaddama kan yarjejeniyar da gwamnatin mulkin sojin Nijar da kuma kamfanin Zimar na kasar Canada suka sanya wa hannu ta samar da babbar matatar mai a yankin Dosso na kasar.
5. Gwamnatin mulkin sojin Guinea ta kaddamar da wani rangadi na fadakar da al'ummar kasar kan daftarin sabon kundin tsarin mulki da aka kwaskware.
✍Ku bayyana mana ra'ayoyinku akan wadannan rahotannin a nan. Za mu karanto wasu daga cikinsu kai tsaye.
Za ku iya sauraron shirin a nan shafinmu na Facebook
Shirin Yamma na 12/11/2024🎤
Masu bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta ina muku barka da wannan lokacin.
Musa Tijjani Ahmad ne zai kasance da ku a shirinmu na maraice da karfe bakwai agogon Najeriya da Nijar, shida kenan agogon GMT da Ghana.
Ku latsa nan domin sauraronmu kai tsaye a babban shafinmu na intanet da zarar lokacin yayi👉🔗 https://p.dw.com/p/15bt5
Ga jerin rahotannin da shirin ya kunsa.
1. Manyan jam'iyyun siyasar Jamus sun amince a gudanar da zaben wuri a ranar 23 ga watan Fabrairun shekara mai kamawa ta 2025.
2. Gwamnatin jihar Kebbi ta shirya wata babbar tawaga zuwa Abuja domin ganawa da shugaban hafsan tsaro don dakatar da ayyukan Lakurawa a jihar.
3. Al'ummar yankin Ogoni da ke kudancin Najeriya sun nuna farin ciki kan matakin gwamnatin Najeriya na karrama jagoran fafutukar yankin Ken Saro-Wiwa da kuma wasu mutum takwas.
4. An fara takaddama kan yarjejeniyar da gwamnatin mulkin sojin Nijar da kuma kamfanin Zimar na kasar Canada suka sanya wa hannu ta samar da babbar matatar mai a yankin Dosso na kasar.
5. Gwamnatin mulkin sojin Guinea ta kaddamar da wani rangadi na fadakar da al'ummar kasar kan daftarin sabon kundin tsarin mulki da aka kwaskware.
✍Ku bayyana mana ra'ayoyinku akan wadannan rahotannin a nan. Za mu karanto wasu daga cikinsu kai tsaye.
Za ku iya sauraron shirin a nan shafinmu na Facebook 👂