Rahotanni daga Najeriya sun ce an yi musayar wuta na dogon lokaci tsakanin sojojin Najeriya da tawagar 'dan ta'adda Bello Turji a Gatawa dake Jihar Sokoto.
Rahotanni sun ce tun karfe 6 na safe ake jin aman wuta a garin har zuwa kusan karfe 3 na ranar yau.
Wani shaidar gani da ido ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar basu taba ganin irin wannan musayar wutar ba, kuma har zuwa lokacin da yake magana ana ta artabu tsakanin bangarorin biyu.
Ko a karshen mako sanda sabon shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya ziyarci yankin inda ya tattauna da dakarun dake aikin tabbatar da tsaro a Tangaza da Ilela a kan muhimmancin murkushe duk wani ɗan ta'adda cikin su harda Bello Turji.