Upgrade to Pro

A yanzu haka dai hankalin 'yan arewacin Najeriya mazauna garin Abavo da ke jihar Delta ya kwanta, biyo bayan janye wa'adin da ake zargin masarautar garin ta ba su na kwanaki hudu da su fice daga garin, saboda yawaitar matsalar sace-sacen jama'a da ta addabi yankin.

Janyewar wannan wa’adi dai ta biyo bayan kwarmata lamarin da 'yan arewar suka yi a sashen Hausa na BBC, abin ya kai ga kunnen fadar shugaban Najeriyar, da gwamnan jihar ta Delta, da shugaban ƙaramar hukumar Ika ta Kudu, da Haɗakar ƙungiyoyin kare fararen hula na arewacin Najeriya ta CNG, na shiga tsakani.

Sarkin Hausawan garin na Abavo, Usman Alasan ya shaidawa BBC cewar “mun yi sallah lafiya ranar juma’a babu wanda ya ce mana kanzil, gwamnan jihar ya turo mana wakilai don jin halin da muke ciki, sannan aka tura DPO ya je wajen sarakunan yankin, inda kuma ya dawo ya sanar da su cewar an janye wannan wa’adi da aka ba su''

Sarkin Hausawan garin na Abavo ya ce “Dukkan ɓangarorin an yi kira garesu tare da jan hankalinsu da dukkan su zauna da juna lafiya ba tare da wata fargaba ba” inji shi.
A yanzu haka dai hankalin 'yan arewacin Najeriya mazauna garin Abavo da ke jihar Delta ya kwanta, biyo bayan janye wa'adin da ake zargin masarautar garin ta ba su na kwanaki hudu da su fice daga garin, saboda yawaitar matsalar sace-sacen jama'a da ta addabi yankin. Janyewar wannan wa’adi dai ta biyo bayan kwarmata lamarin da 'yan arewar suka yi a sashen Hausa na BBC, abin ya kai ga kunnen fadar shugaban Najeriyar, da gwamnan jihar ta Delta, da shugaban ƙaramar hukumar Ika ta Kudu, da Haɗakar ƙungiyoyin kare fararen hula na arewacin Najeriya ta CNG, na shiga tsakani. Sarkin Hausawan garin na Abavo, Usman Alasan ya shaidawa BBC cewar “mun yi sallah lafiya ranar juma’a babu wanda ya ce mana kanzil, gwamnan jihar ya turo mana wakilai don jin halin da muke ciki, sannan aka tura DPO ya je wajen sarakunan yankin, inda kuma ya dawo ya sanar da su cewar an janye wannan wa’adi da aka ba su'' Sarkin Hausawan garin na Abavo ya ce “Dukkan ɓangarorin an yi kira garesu tare da jan hankalinsu da dukkan su zauna da juna lafiya ba tare da wata fargaba ba” inji shi.